(ABNA24.com) Dan majalisar dokokin tarayyar Najeriya mai wakiltar Rano da Bunkure, Alhaji Kabiru Alhassan ne ya fadawa ‘yan jarida labarin mutuwar sarkin.
Rahotanni daga masarautar da ta ke jahar kano sun ce tun a shekaran jiya juma’a ne aka kwantar da sarkin a asibitin Nasarawa da ke cikin birnin kano, kafin daga baya a mayar da shi zuwa asibitin koyarwa na Malam Aminu Kano, inda Allah ya yi masa rasuwa.
Sarkin na Rano ya rasu yana dan shekaru 74 kuma ya bar mata biyu da ‘ya’yan 17.
Masarautar Rano tana daga cikin sabbin masarautu hudu da gwamnatin kano a karkashin Dr. Abdullahi Umar Ganduje ta kirkiro.
/129
4 Mayu 2020 - 03:41
Lambar labari: 1033094
Masarautar Rano da ke jahar kano ta sanar da rasuwar sarki Dr. Abubakar Ila na biyu, a jiya Asabar.